Hisbah ta Kano ta kama mutane 22 da ake zargin suna canza jinsinsu ta hanyar saka sutura

  • Hukumar ta ce an kama mutanen ne a wurare daban-daban na Kano bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga mazauna jihar.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama mutane 22 da ake zargin masu canza jinsi ne ta hanyar sutura a yayin wasu samame da ta gudanar a wurare daban-daban na jihar.

Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar da kamen, yana mai cewa an kama waɗanda ake zargin ne a yankunan Zoo Road, Court Road da wasu wuraren da ke maƙwabtaka da su.

A cewarsa, akasarin waɗanda aka kama sun shigo Kano ne daga wasu jihohin.

Ya ce waɗanda aka kama sun haɗa da mata 10 da maza 12, kuma sun amince cewa suna gudanar da ayyukan neman abokan hulɗa ta yanar gizo da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi.

Aminuddeen ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci hukunci bisa doka.

Mataimakin Kwamanda Janar ɗin ya sake jaddada cewa Hisbah ba za ta lamunci ayyukan da ta bayyana a matsayin lalata ko rashin ɗa’a a Kano ba, yana mai cewa hukumar za ta ƙara tsaurara matakan daƙile irin waɗannan ayyuka.

ArewaHisbahKano
Comments (0)
Add Comment