Plateau ta rufe makarantu saboda ɓarkewar cutar diphtheria

  • Gwamnatin jihar ta ce matakin na da nufin daƙile yaɗuwar cutar tsakanin yara, yayin da adadin waɗanda ake zargin sun kamu ya kai 148.

Gwamnatin Jihar Plateau ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na wucin gadi daga ranar Litinin, 7 ga Satumba, a wani mataki na daƙile yaɗuwar cutar diphtheria da ta ɓulla a jihar.

Gwamna Caleb Mutfwang ne ya bayar da umarnin ranar Asabar, kuma za a ci gaba da rufe makarantun har sai gwamnati ta ba da wani sabon umarni.

Aƙalla mutane 23 ne suka mutu a Plateau sakamakon ɓarkewar cutar, wadda ta fara yaɗuwa a jihar tun farkon watan da ya gabata.

Da yake magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) ranar Juma’a, Kwamishinan Lafiya na jihar, Nicholas Baamlong, ya ce an samu mutane 148 da ake zargin sun kamu da cutar.

Ya ce a halin yanzu ana kula da marasa lafiya takwas a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUTH), yayin da wasu biyar ke karɓar magani a Asibitin Ƙwararru na Plateau, inda aka kafa cibiyoyin killace masu ɗauke da alamun cutar.

Baamlong ya ce gwamnatin jihar ta sanar da Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) game da ɓarkewar cutar tare da neman kayan aikin da ake buƙata domin ɗaukar samfura da jigilar su zuwa ɗakin gwaje-gwaje domin tabbatar da cutar.

Ya ce jihar ta riga ta samu kayan aikin da jami’an lafiya ke buƙata domin ɗaukar samfura daga mutanen da ake zargin sun kamu da cutar da kuma aika su domin gwaji.

Kwamishinan ya bayyana damuwa kan ƙarancin maganin diphtheria antitoxin a Najeriya.

Ya kuma buƙaci iyaye su tabbatar da cewa yaransu sun karɓi dukkan alluran rigakafin da ake buƙata kuma sun kammala tsarin rigakafin.

Ya ce wasu daga cikin yaran da cutar ta shafa ba su samu rigakafin ba, yayin da wasu kuma ba su kammala karɓar alluran rigakafin ba.

Baamlong ya shawarci iyaye da masu kula da yara da su gaggauta kai su asibiti idan suka fara nuna alamun cutar, yana mai cewa wasu daga cikin mutanen da suka mutu sun makara wajen zuwa cibiyoyin lafiya.

Ya ce gwamnati ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da kuma gudanar da allurar rigakafi a yankunan da cutar ta fi ƙamari domin daƙile yaɗuwarta.

Ya kuma buƙaci mazauna jihar su kula da tsaftar jiki da muhalli, tare da kauce wa cunkoso domin rage yiwuwar yaɗuwar cutar.

Kwamishinan ya ce ana ci gaba da tuntuɓar hukumomin makarantu saboda damuwar cewa sake buɗe makarantu na iya ƙara yawan cuɗanya tsakanin yara, lamarin da ka iya taimakawa wajen yaɗa cutar.

Diphtheria cuta ce da ƙwayar cuta ke haddasawa wadda galibi ke shafar hanyoyin numfashi na sama, sannan a wasu lokuta ta kan shafi fata.

Cutar na iya samar da guba wadda ke lalata zuciya da jijiyoyin ƙwaƙwalwa.

Ana iya kare mutum daga cutar ta hanyar rigakafi, sai dai ana buƙatar allurai da dama da kuma ƙarin allurar kariya domin samar da dawwamammiyar kariya.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), diphtheria na iya yin sanadin mutuwar kusan kashi 30 cikin 100 na waɗanda suka kamu da ita idan ba a ba su kulawar da ta dace ba, musamman yara ƙanana.

DiphtheriaNCDCPlateau
Comments (0)
Add Comment