- Ireland da Spain na jagorantar kiraye-kirayen taƙaita shigo da kayayyakin da ake samarwa a matsugunan Isra’ila daga yankin Yammacin Kogin Jordan
Ministocin harkokin wajen Tarayyar Turai (EU) sun kasa cimma matsaya guda kan shirin sanya takunkumin ciniki kan kayayyakin da ake shiga da su daga matsugunan Isra’ila da ke yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, yayin da ake samun ƙaruwar tashe-tashen hankula da cin zarafin Falasɗinawa a yankin.
Ireland, wadda ke riƙe da shugabancin majalisar EU a halin yanzu, ta karɓi baƙuncin taron ministocin harkokin wajen ƙasashen ƙungiyar a Wicklow ranar Talata da Laraba, kamar yadda Al Jazeera ta ruwaito.
Rahoton Al Jazeera ya ce Ireland da Spain, tare da goyon bayan Belgium da Netherlands, sun jagoranci kira ga ƙungiyar EU da ta sanya takunkumin shigo da kayayyakin da ake samarwa a matsugunan Isra’ila da ake kallonsu a matsayin haramtattu a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa.
Sai dai Jamus, Austria, Czechia da Hungary sun nuna adawa da duk wani yunƙuri na sanya irin wannan takunkumi, suna masu cewa hakan na iya lalata hanyoyin diflomasiyya da Isra’ila.
Ireland ta kasance ƙasa ta farko a EU da ta haramta shigo da kayayyakin da ake samarwa a matsugunan Isra’ila. Ƙasar ta amince da Falasdinu a matsayin ƙasa a shekarar 2024, sannan ta ci gaba da sukar faɗaɗa matsugunan Isra’ila a yankin Yammacin Kogin Jordan.
Haka kuma, Dublin ta nemi a sake duba yarjejeniyar EU da Isra’ila ta haɗin gwiwa, wadda aka ƙulla a shekarar 2000 kuma take zama ginshiƙin hulɗar kasuwanci tsakanin ɓangarorin.
“Ya kamata mu kasance muna ɗaukar mataki tare… Ba abin yarda ba ne mu ce muna son mutunta dokokin ƙasa da ƙasa a wani ɓangare, amma ba mu yi hakan a wani ɓangaren ba,” in ji ministar harkokin wajen Ireland, Helen McEntee.
Lynn Boylan, ƴar majalisar Tarayyar Turai daga Ireland, ta shaida wa Al Jazeera cewa Ireland ce kaɗai ta gabatar da batun matsugunan Isra’ila yayin taron ministocin harkokin wajen da aka gudanar a Wicklow.
Babbar jami’ar manufofin harkokin wajen EU, Kaja Kallas, ba ta yi bayani kai tsaye kan yiwuwar sanya takunkumin cinikin ba bayan taron.
A wani taron ministocin EU da aka gudanar a Brussels a watan Yuli, Kallas ta ce ministocin sun tattauna hanyoyi uku da suka haɗa da tsarin lasisin shigo da kayayyaki, ƙarin haraji mai tsauri ko kuma dakatar da shigo da kayayyakin baki daya, kamar yadda Reuters ta rawaito.
Ta ce a wancan lokaci, shirin dakatar da shigo da kayayyakin ne ya samu goyon baya mafi yawa, amma ba a samu cikakken rinjaye kan ɗaya daga cikin zaɓukan ba.
EU ita ce babbar abokiyar kasuwancin Isra’ila, inda cinikin kayayyaki tsakanin ɓangarorin ya kai kusan dala biliyan 50 a shekarar da ta gabata, bisa bayanan da Al Jazeera ta ambato.
Har ila yau, ana ci gaba da muhawara kan ko takunkumin cinikin zai buƙaci amincewar dukkan ƙasashen EU ko kuma za a iya amincewa da shi ta hanyar ƙuri’ar mafi rinjaye.
A yayin taron, masu zanga-zanga sun gudanar da gangami a kusa da wurin shaƙatawa na wasan golf da aka gudanar da taron, inda suka riƙe allunan da ke ɗauke da saƙonni kamar “Ya kamata ku ƙaurace wa Isra’ila yanzu” da kuma “A sanya wa Isra’ila takunkumi”.
Madogara: Al Jazeera