IPMAN: Gidajen mai za su rage farashin fetur cikin kwanaki masu zuwa

Dillalan man fetur sun ce za su sake duba farashin famfunan mai da zarar sabbin kayayyakin fetur sun fara shigowa kasuwa.

Ƙungiyar Dillalan Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN) ta ce gidajen mai da ke faɗin Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja, za su fara rage farashin fetur a famfunan mai cikin ƴan kwanaki masu zuwa.

Sakataren Yaɗa Labarai na Ƙasa na IPMAN, Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Abuja ranar Alhamis.

Ukadike ya ce ƴan kasuwar na shirin sake duba farashin man fetur da dabarun sayar da shi, yayin da sabbin kayayyakin fetur ke shirin shigowa kasuwa.

Ya ce shigowar sabbin kayayyakin na iya haifar da sauye-sauye a kasuwar man fetur, inda ƴan kasuwar za su ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa masu amfani sun ci gaba da samun kayayyakin da suke buƙata.

Sai dai kakakin IPMAN ya ce har yanzu ba a tabbatar da takamaiman lokacin da sabbin kayayyakin za su iso ba, saboda ƴan kasuwar ba su samu tabbatacciyar ranar fara shigowarsu ba.

Ya ce duk wani sauyi zai kasance ne bisa ƙa’idoji da dokokin da ake amfani da su.

“Da zarar sabbin kayayyakin sun fara shigowa, ana sa ran ƴan kasuwa za su yi gaggawar sake duba farashinsu tare da sabunta kayayyakin da suke bayarwa,” in ji Ukadike.

“Bayan wannan tsari, idan muka fara sayayya gobe ko jibi, da zarar an fara, za mu daidaita farashinmu sannan mu fara samar da sabon kayan ga masu amfani.

“Sayen man na iya farawa cikin ƴan kwanaki, ya danganta da lokacin da aka fara aiwatar da tsarin a hukumance.”

Ya ce ana sa ran ci gaban zai sake haifar da sauye-sauye a kasuwa yayin da tashoshin mai ke daidaita farashinsu tare da samar da sabbin kayayyakin ga masu amfani.

Kamfanin matatar man Dangote ya ƙara farashin man a wajen sari da ₦65 kan kowace lita, daga ₦1,200 zuwa ₦1,265, daga ranar 29 ga watan Agusta.

Wannan shi ne karo na uku da matatar ta sanar da ƙarin farashi cikin kwanaki takwas, lamarin da daga bisani ya bayyana a farashin da ake sayar da fetur a gidajen mai.

IPMANMan FeturNajeriya
Comments (0)
Add Comment