Trump ya ba da shawarar sauya sunan Mashigin Ruwan Hormuz zuwa “Trump Strait”

  • Shugaban Amurkan ya daga baya rage muhimmancin shawarar yayin da fada da Iran ke ci gaba

Shugaban Amurka Donald Trump ya ba da shawarar sauya sunan Mashigin Ruwan Hormuz zuwa “Trump Strait”, duk da cewa ana ci gaba da gwabza faɗa tsakanin Amurka da Iran a kusa da wannan muhimmin mashigin ruwa.

Trump ya gabatar da shawarar ne ranar Laraba a shafinsa na Truth Social, yayin da yake cewa Amurka ce ke da cikakken iko kan mashigin ruwan.

“Yanzu da yake ƙarƙashin ikon Amurka, ya kamata mu sauya sunan Hormuz Strait zuwa Trump Strait??? Kamar Amurka kanta, zai kasance ‘mai zafi’ fiye da kowane lokaci!” Trump ya rubuta.

Daga baya fadar White House ta wallafa taswirar yankin Gulf a shafukan sada zumunta, inda ta yi amfani da sunan da Trump ya gabatar, tare da cewa, “Sunan yana da daɗin ji.”

A cikin makonnin baya-bayan nan, Trump ya sha yin barazanar cewa Amurka za ta mallaki Mashigin Ruwan Hormuz, har ma ya wallafa taswirar da ke nuna mashigin a matsayin wani sabon yankin Amurka.

Sai dai daga baya ya rage muhimmancin batun sauya sunan.

Lokacin da wani ɗan jaridar AFP ya tambaye shi a Ofishin Oval ko gaske yake kan sauya sunan, Trump ya amsa cikin dariya cewa, “An dai jefo shawarar yin hakan ne.”

Trump ya taɓa gabatar da wasu shawarwarin sauya sunayen wurare da aka fara ɗauka a matsayin barkwanci kafin daga bisani wasu daga cikinsu su zama manufofin gwamnati.

A makon da ya gabata, ya rattaba hannu kan wata doka ta sauya sunan Lake Ontario zuwa “Lake America” yayin da ake fama da taƙaddamar kasuwanci da maƙwabciyar ƙasar Canada, kamar yadda AFP ta rawaito.

A watan Janairun 2025, Trump ya kuma sauya sunan Gulf of Mexico zuwa “Gulf of America”. Mexico da Canada ba su amince da waɗannan sauye-sauyen sunaye ba.

Trump ya kuma shiga cikin wasu sauye-sauyen sunaye da suka shafi cibiyoyin Amurka, ciki har da Kennedy Arts Centre da ke Washington.

A ranar Laraba, Ma’aikatar Baitulmalin Amurka ta kuma fitar da tsabar dala guda da ke ɗauke da hoton Trump domin tunawa da cikar Amurka shekaru 250 da samun ƴancin kai, a cewar AFP.

Mashigin Hormuz na ci gaba da kasancewa cibiyar rikicin Iran

Shawarar Trump ta zo ne a yayin da yaƙi da Iran ke ci gaba da kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kasuwannin makamashi na duniya.

Sojojin Amurka sun kaddamar da sabbin hare-hare kusa da Mashigin Ruwan Hormuz ranar Talata, bayan Trump ya ce Iran na kokarin sake shimfida nakiyoyi a mashigin.

Iran ta ce ɗaya daga cikin hare-haren Amurka ya kashe mutane huɗu a wani taron aure, inda ta bayyana harin a matsayin “laifin yaƙi”.

Daga baya Tehran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin Amurka da ke Jordan, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait, Bahrain da Iraq.

Yaƙin ya kuma taimaka wajen kara farashin man fetur a Amurka tare da jefa jam’iyyar Republican ta Trump cikin matsin siyasa gabanin zaɓen tsakiyar wa’adi na watan Nuwamba.

Mashigin Ruwan Hormuz na daga cikin muhimman hanyoyin jigilar makamashi a duniya, inda kusan kashi ɗaya bisa biyar na man duniya ke bi ta wurin yau da kullum.

A cewar AFP, Iran ta taƙaita zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin sakamakon yaƙin.

Trump ya ce a ranar Laraba Amurka na da shirin sake kai wa Iran hari, yayin da ya ƙara da cewa yaƙin da aka sabunta ba zai daɗe “sosai” ba.

“An kai hari mai tsanani a daren jiya, kuma a shirye muke mu sake kai wani a duk lokacin da muka ga dama,” Trump ya shaida wa manema labarai a Ofishin Oval.

Madogara: AFP

AmurkaHormuzIranTrump
Comments (0)
Add Comment